Potiskum: An kai hari a kusa da fadar Sarkin Fika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani hari da aka kai Yobe a watannin baya

Rahotanni daga Potiskum a jihar Yoben Nijeriya na cewa wani dan kunar bakin wake a tayar da bam, inda ya kashe kansa, ya kuma kashe karin wasu mutane tare da jikkata wasu.

Lamarin ya auku ne babban masallacin Juma'a dake fadar Sarkin Fika a garin na Potiskum.

Kwanakin baya an kai hari makamancin wannan a masallacin dake fadar Mai martaba Shehun Borno, inda nan ma aka samu asarar rayuka.

Jihohin Barno da Yode dai suna fama da hare-hare cikin 'yan shekarun nan.