Dakarun Syria na yunkurin kutsa kai cikin Aleppo

Wani sojan Free Syrian Army a Aleppo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani sojan Free Syrian Army a Aleppo

Kungiyoyin ’yan adawar Syria sun ce dakarun gwamnati na amfani da jiragen sama da tankokin yaki a Aleppo a yunkurinsu na kutsa kai cikin gundumar Salaheddin mai muhimmanci wadda ke hannun 'yan tawaye.

Gundumar dai na kan hanyar shiga tsakiyar birnin na Aleppo ne.

Majiyoyin soji a kasar ta Syria sun ce yanzu haka an girke dakaru dubu ashirin a ciki da kewayen birnin, wanda shi ne birni mafi girma a kasar.

Sai dai kuma wani kakakin ’yan tawayen ya ce suna ci gaba da nausawa zuwa tsakiyar birnin:

“Yanzu haka sojojin Free Syrian Army ne ke iko da fiye da kashi saba'in cikin dari na Aleppo, sun kuma dumfari wani gini na tarihi mai cikakken tsaro da ke tsakiyar tsohon birnin”, inji shi.

Karin bayani