Firayim Ministan Syria ya sauya sheka

Riyad Hijab Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayim Ministan Syria Riyad Hijab

Firayim Ministan Syria, Riyad Hijab ya sauya sheka kuma ya tsere zuwa Jordan tare da iyalansa.

Sauyin shekar tasa dai na nuna cewa irin girman barakar da aka samu a gwamnatin Bashar al-Assad ta zarta a tsakanin sojoji.

Wani kakakinsa, Muhammad Itri, ya karanta wata sanarwa daga gareshi dake cewa, ya bar abin da ya kira gwamnati ’yar ta'adda, ya bi sahun masu kokarin yin juyin-juya-hali.

Kakakin ya kara da cewa soja ne da ya taka rawa a juyin-juya-halin kasar, amma ya juya wa wannan gwamnati baya saboda kasha-kashe da nakasa jama'a da kuma ta'addancin da ke aikatawa.

“Ina [yi wa al’ummar Syria] wannan jawabi ne a daidai wannan lokaci da kasar ke cikin wani mummunan yanayi na kisan kare-dangi da kisan rashin imani da ake aikatawa a kan fararen hular da ba sa dauke da makamai, wadanda kawai suke neman a ba su ’yanci, a kuma rika mutunta su”, inji shi.

Ya kuma ce “A yau ina shaida wa talakawan Syria cewa na sauya sheka daga gwamnatin 'yan ta'adda mai kashe jama'a, na shiga sahun juyin-juya-hali mai tsarki”.

Mista Itri ya ce Firayim Ministan ya shirya sauya shekar ne tun sama da watanni biyu da suka wuce, a lokacin da aka dora shi a kan mukamin.

Ya ce tilasta masa karbar mukamin Shugaba Assad ya yi, yana cewa ko dai ya karba ko kuma a kashe shi.

Ana kallon Mista Riyad Hijab a matsayin mai goyon bayan jam'iyyar Ba’ath, wanda za a iya dogaro da shi a lokacin da ake cikin matsala.

Sai dai kuma shi Sunni ne, ba Alawi ba—’yan tsiraru masu rike da ragamar iko.

Wadansu majiyoyin ’yan adawa na cewa Hijab da iyalinsa da ma, mai yuwuwa, wadansu karin ministocin biyu sun tsallaka kan iyaka sun shiga kasar Jordan.

Sai dai kuma sun ce an kama Ministan Kudi Muhammad Jalilati a lokacin da shi ma yake kokarin tserewa.

Amma kuma gwamnatin Assad na kokarin nuna al’amarin ta wata fuska, ta hanyar fitar da wata doka dake nuna cewa an kori Mista Hijab daga mukaminsa, ba tare da bayar da dalili ba.

An kuma bayar da sanarwar nada Dokta Omar Ghalawanji a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Gidan talabijin na kasar ne ya bayar da wannan sanarwa ta kora a daidai lokacin da ake bayar da labarin tashin bam a hawa na uku na ginin gidan talabijin din a Damascus.

Bam din bai haddasa barna mai yawa ba, ya dai raunata mutane uku.

Tuni dai wani kakakin gwamnatin Jordan ya tabbatar da isar Riyad Hijab kasar.

Karin bayani