An cimma matsaya kan jayayyar harajin man Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani sojan Sudan ta kudu yana tsaron wata matatar mai a jahar Unity

Mai shiga tsakani na kungiyar tarrayyar Afrika a rikicin Sudan Thabo Mbeki ya bayarda sanarwar cewar an cimma yarjejeniya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu dangane biyan kudin fiton mai; bayan kwashe watanni ana zazzafar jayayya wadda ta kusan kai kasashen biyu ga gwabza yaki.

Mr.Mbeki ya sanarda hakan ne ga y'an jarida da sanyin safiyar assabar a babban birnin kasar Ethiopia watau Adis Ababa, inda aka jima ana tattaunanawa tsakanin wakilan kasashen.

Yace an warware dukkanin batutuwan ke jawo kace-nace ciki har da batun ko nawa Sudan ta Kudu zata biya domin aike wa da danyen man ta cikin kasar Sudan.

Sai dai bai yi wani karin bayani ba, kuma babu daya daga cikin kasashen biyu da ta ce kala kan batun ya zuwa yanzu.

Mafari

Kasar Sudan ta Kudu dai ta dakatarda hako danyen man nata ne a watan Janairu sakamakon rashin jittuwa da gwamnatin Khartoum kan kudin harajin da zata rika karba idan aka shiga da man ta cikin yankin ta, abinda ya kara zurfafa matsalolin tattalin arziki da dama bangarorin biyu ke fama dasu.

Takaddama kan fitar da danyen man dai daya ce daga cikin batutuwa da dama da kasashen biyu ke jayayya akai cikin har da na tsaro, da shata kan iyakoki, da kuma batun wanene dan wace kasa; ababen da suka kawo tsamin danganta tsakanin kasashen biyu tun bayan da Sudan ta Kudu ta aiyana 'yanci kanta daga Sudan fiye shekara dayan ta wuce.

Majalisar dinkin duniya dai tayi barazanar saka musu takunkumi idan ba a samu cimma matsaya ba.

Karin bayani