Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniya akan mai

sudan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Man Sudan ta Kudu zai fara bi ta Sudan

Bayan shafe lokaci mai tsawo ana jan'in-ja, yanzu dai a cimma yarjejeniya tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

Sudan ta Kudu za ta biya makwabciyarta jamhuriyar Sudan dala biliyon uku a matsayin diyya saboda hasarar da Sudan din tayi na rijiyoyin mai sakamakon raba kasar.

Har ila yau, an cimma matsaya akan kudaden da za a dunga baiwa Sudan din a matsayin kudin hanya saboda bututan mai da zasu bi ta Khartoum zuwa cikin teku.

Ministan yada labaran Sudan ta Kudu, Barnaba Benjamin ya bayyana matakin a matsayin ci gaba mai ma'ana, kuma nan bada jimawa ba zasu fara fitar da danyen mai zuwa kasashen waje.

Sai dai kuma wannan yarjejeniyar da aka cimma a kasar Ethiopia zata fara aiki ne kawai, idan aka warware takadamma akan batun kan iyakokin kasashen biyu da kuma tsaro.

Kungiyar tarrayar Afrika AU ta shaidawa BBC cewar zai a koma teburin tattaunawa a karshen wannan watan inda shugabannin kasashen biyu zasu rattaba hannu a yarjejeniyar.

Karin bayani