Syria: Burtaniya tayi maraba da kudurin Majalisar Dinkin Duniya

Image caption Sakataren harkokin wajen Burtaniya Williams Hague

Sakataren harkokin Wajen Burtaniya Willianms Hague yayi marhabin da da kudurin da majalisar dinkin duniya da ammince dashi a jiya wanda yayi tir da tashin hankalin da akeyi a Syria tare da neman a sauya gwamnati a kasar.

Mr. Hague yace wannan ya aike da wani sako karara cewar duniya tayi kai daya wajen yin tir da abinda ya kira ''keta hakki bil adama da gwamnatin Syria keyi''kuma ta (duniyar) bukaci ta dauki mataki farko na kawo karshen fadan.

Sai dai kuma wakiliyar BBC a Majalisar Barbara Plett tace duk da gagarumin goyon bayan da aka baiwa kudurin babu yiwuwar ya kawo wani sauyi a matakin da gwamnatin Syria ke dauka, saboda kudurin babban taron majalisar ba abu ne da ya zama wajibi ayi aiki dashi ba bisa doka.

Amma kuma kasashen yamma na fatan wannan gagarumi goyon bayan zai kara matsawa kasashen Rasha da China lamba wadanda suka hau kujerar naki a kudurorin kwamitin tsaro na Majalisar wadanda aiki dasu ya zama wajibi.

Matsayin Rasha da China

Kasashen biyu dai na daga cikin kasashen 'yan kalilan da suka ki baiwa kudurin na jiya goyon baya.

A maimakon haka ma sai suka yi tir dashi sun cewar ya dora laifi ne kawai kan bangare daya a fadan tare da nuna cewar sunanan kan bakar su.

Karin bayani