Dan kunar bakin wake ya kaiwa jami'an tsaro hari a Damaturu

hari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin da aka kaiwa 'yan sanda a Yobe

A Damaturu babban birnin jihar Yobe dake arewacin Najeriya, wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a kusa da motar jami'an tsaro, inda ya hallaka kansa da kuma wasu daga cikin jami'an tsaron na hadin gwiwa wato JTF.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe, Patrick Egbuniwe ya tabbatar da afkuwar lamarin, amma bai bayyana adadin wadanda harin ya rutsa dasu ba.

Wata maata a Unguwar Low Coast ta shaidawa BBC cewar lamarin ya janyo firgice a tsakanin al'umma a yayinda mutane suka shige gidajensu.

Kawo yanzu babu kungiyar data amsa cewar itace ta kai harin, amma dai kungiyar Boko Haram tana yawan kai hare hare a jihar Yobe, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Wannan harin kunar bakin waken na zuwa ne kwanaki biyu bayan da aka nufi Sarkin Fika da wani harin kunar bakin wake, amma Allah ya kubutardashi.

Karin bayani