'yan fashin teku sun kashe sojan ruwan Najeriya 2

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mayakan sa-kai a yankin Neja Delta na Najeriya

Rundunar sojan ruwan Najeriya tace an kashe wasu mayakan ruwan kasar su 2 aka kuma sace wadansu 'yan kasashen waje 5 a cikin wani harin da aka kaiwa wani jirgin ruwan dakon mai a tekun da ke daura da idan ake hakar danyen mai a kasar.

Rundunar tace 'yan bindiga dadi ne suka kaiwa jirgin hari ranar assabar a wani wuri mai tazarar tafiyar nautical Miles 30 daga gabar teku.

Wani kakakin rundunar Kabir Aliyu ya shaidawa BBC cewar jirgin ruwan mallakar wani kanfanin kwangilar sarrafa man fetur da gas, ya dauki sojojin ruwan Najeryar ne domin bashi kariya.

Ko baya ga kashe 2 daga cikin sojan ruwan haka kuma an raunata wasu biyu.

Sace 'yan kasashen waje

Ya ce maharan sun yi awon gaba da wasu 'yan kasashen waje biyar wadanda suka fito daga kasashen indonesiya, da Thailand, da Malaysia da kuma Iran.

Rundunar sojan ruwan dai ta aike da wani jirgi mai saukar ungulu da kuma wani babban jirgin ruwa zuwa inda lamarin ya faru domin farautar 'yan fashin.

Wannan lamarin zai zama babban abin damuwa ga masana'atar hada-hadar danyen mai da gas ta Najeriya.

Yankin da lamarin ya faru dai yana da tarihin sace mutane a baya.

A yayinda wani shirin yiwa mayaka afuwa ya kawo lafawar lamurran, sace 'yan Najeriya a yankin Neja Delta ya kai wani mataki na la-haula.

Fashi a teku dai na karuwa a sassa daban-daban na Afrca ta yamma.

Ofishin hukumar kula da zirga-zirgar teku ta duniya yace ya samu bayannan kai hare-haren 'yan fashin teku sau 17 a Najeriyar a farkon wannan shekara, abin da ke nuna lamarin ya karu sosai idan aka kwatanta da bara.

Karin bayani