'Sojan Syria sun yiwa y'an tawaye mummunan ta'adi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bakin hayaki ya turnuke birbishin unguwar Salah-al-din ta birnin Aleppo yayinda ake gwabza fada.

'Yan tawaye a Aleppo birni na biyu mafi girma a kasar Syria sun ce sojojin gwamnati sun yi musu ruwan bama-baman da ba su taba ganin irinsa ba tun lokacinda aka fara fadan makonni biyu da suka gabata.

Wani takaitaccen labarin kada-ta-kwana da gidan tallabijin din kasar ya nuna yace dakarun gwamnatin sun yi mummunan ta'adi akan wadanda ya kira 'yan ta'adda a unguwar Saleheddin dake kudu maso yammacin birnin da kuma wasu unguwannin da ke kusa da wurin.

Gidan tallabijin din yace wadanda ba a kashe ba daga cikin mayakan 'yan tawayen da ke unguwar sun mika kai.

Kafin fitowar wannan labarin dai wani faifan bidiyo da masu fafutuka suka saka a shafin internet ya nuna yadda ake yiwa unguwanin luguden wuta da bindigigon artilery.

Karin bayani