'yan bindiga sun hallaka sojoji 5 a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Ivory Coast Alasane Ouattara ya zantawa da 'yan jarida

Wasu mahara a kasar Ivory coast sun kashe sojoji biyar a lokacinda suka kaiwa wani caji ofis da wani wurin bincike na soji hari a Abdjan babban birnin kasar.

Maharan sun sanya kayan soji kuma sun yi amfani ne da bindigogi masu sarrafa kansu.

Ba a tantance dalilan da suka sanya su kai wannan hari ba.

An yi harbe-harben ne a yankin Yopogon wurinda aka yi mummunan fada na kwatar ikon da birnin na Abidjan a bara lokacinda aka yi rikicinda ya biyo bayan zaben kasar.

Karin bayani