An yi arangama tsakanin matasa da masu kishin Islama a Mali

Arangama tsakanin masu zanga zanga da masu kishin Islama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arangama tsakanin masu zanga zanga da masu kishin Islama

Daruruwan matasa 'yan kasar Mali ne suka yi wata taho mu gama da masu kishin islama dake iko da yankin a wata zanga-zangar adawa da tursasa musu amfani da shari'ar musulunci.

An gudanar da zanga-zangar ne a birnin Gao, bayan da masu kishin islaman suka sanar da shirin su na yanke hannun wani barawo.

Dakarun da ke iko da yankin sun yi harbi a sama domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Mutane da dama ne suka samu raunuka a zanga-zangar, ciki har da wani dan jarida da 'yan bindiga suka daka saboda ya sanar da shirin yanke hannun barawon a Radiyo.mali

Karin bayani