An rushe shagunan 'yan kasuwa a Jos, Najeriya

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na cewa dimbin 'yan kasuwa sun wayi gari ranar Litinin sun tarar hukumomi sun rusa masu shaguna da rumfunan kasuwancinsu cikin daren jiya, inda wasunsu ba su ma samu hajojinsu ba,

Wadansu 'yan kasuwar da al'amarin ya shafa sun yi zargin cewa yayin rushe-rushen an sace musu kanayn hajarsu.

Shugabannin 'yan kasuwa dai sun ce shaguna da aka rusa sun kai kimanin dari shida kuma galibin 'yan kasuwa da lamarin ya shafa masu sayar da kayan abinci da tufafi da kayan kwalliya.

Duk kokarin da wakilin BBC yayi domin jin ta bakin hukumar raya birnin Jos wato JMDB, ko kwamiti na musamman da gwamnati ta kafa domin rusa abinda gwamnatin ke kira gine-ginen da basa bisa ka’ida, ya ci tura.

Shi kuma kwamishinan watsa labarai na jihar Filato, Mista Yiljhap Abraham ya shaidawa BBC cewa a ba shi karin lokaci domin shi ma yana ci gaba da tuntuba da kuma tattaro bayanai kan hakikannin lamarin.