Anyi taro akan tsaro a yankin Sahel

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Malam Bazoum Muhammed, ministan harkokin waje na Niger

Taron ministocin hulda kasashen wajen kasashen yankin Sahel bakwai ya jaddada goyon bayansa ga shirin gwamnatin Mali na tattaunawa da dukkan bangarorin rikicin kasar.

Taron da aka yi a birnin Yamai ya tattauna ne akan sha'anin tsaro a kasashen na yankin Sahel, musamman ma halin da ake ciki a Mali wacce ke fuskantar kalubalen tsaro tun daga watan Aprilun da ya gabata.

Najeriya ma dai na daga cikin kasashen da suka halarci taron.

Tun bayan barkewar rikici a Mali ne dai kasashen na Sahel ke cigaba da nuna damuwa dangane da harkar tsaro a yankin.