BBC navigation

Dan bindiga ya kashe 'yan addinin Sikh 7 a Amurka

An sabunta: 6 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:24 GMT

Wurin ibadar addinin Sikh a Amurka

Wani dan bindiga a jihar Winconsin ta Amurka ya kai hari a wani wurin ibadar mabiya addinin Sikh inda ya kashe a kalla mutane 7 wadanda suka hallara domin yin ibada.

Wadanda lamarin ya faru akan idonsu sun ce an kai harin ne lokacinda masu ibada suka hallara domin addu'oin safe kuma baya ga mutane bakwan da suka mutu; akwai wasu uku da ake yiwa magani a wata asibiti dake can rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.

Rahotanni sun ce mata da yara na daga cikin wadanda ke cikin wurin Ibadar sai dai sun bobboyewa dan bindigar ne a cikin kabat-kabat.

'yan sanda sun ce ya harharbi wani jami'in 'yan sandan da ya fara isa wurin sau da dama, kafin jami'in ya mayarda martani ya kashe dan bindigar.

Ba a san dalili ba

Wasu daga cikin wadanda ke wurin sun ce maharan sun fi daya, amma 'yan sanda sun ce sun yi amannar cewa mutum daya ne ya kai harin.

Hukumomi dai sun ce ba su yada sanin dalilin kai harin ba amma suna jin cewar kuskuren fahimtar ko su waye ne ya haddasa hakan.

Wasu dai na daukar 'yan addinin sikh da cewar musulmi ne saboda al'adarsu ta daura rawani abinda ya sanya suka rika fuskantar hare-hare a Amurka tun bayan harin da kungiyar musulmi masu gwagwarmaya da makamai ta Alkaida ta kai a kasar a ranar sha daya ga watan satumban 2001.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.