Ivory Coast na farautar mahara a Abidjan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawawwakin wasu sojojin da aka kashe a sansanin

Gwamnatin kasar Ivory Coast ta ce tana cigaba da farautar maharan da suka kai hari kan wani babban sansanin Soji dake babban birnin kasuwancin kasar Abidjan a jiya litinin wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane bakwai.

Maharan dai sun ja daga na tsawon lokaci a ciki da kuma zagayen sansanin na tsawon awowi har lokacinda aka kora su baya a dai-dai faduwar rana.

An dai raunata sojoji gwamnati da dama a harin kuma an dauki wasu makamai da albarusai daga sansanin.

Wannan harin dai ya zone bayan kwashe karshen makon da ya gabata ana rikici a birnin inda aka kashe akalla soja hudu a cikin wani harin da aka kaiwa wani chaji ofis da wurin bincike a yammacin garin.

Abinda BBC ta gani

Wakilin BBC John James da ya ziyarci sansanin yace an kayarda babban kyauren kofar sansanin kasa war-was kuma daben dakin masu tsaron kofar rufe yake da jini.

''Akwai gawawwaki kwakkwance a saman ciyawa a sassa da dama na sansanin rufe da wasu zannuwa na leda.''

''Wasu sojojin dai suna cike fushi suna cewar ba a basu isassun makamai, yayinda wasu ke karfafa zaton cewar maharan wadanda suka san yadda sansanin yake daga ciki ne.''

A wajen sansanin, mazauna garin da ke kusan dashi suna cikin firgita bayan karar harbe-harben ta tayarda su daga barci da misalin karfe ukku da rabi na dare.

Daukin da wasu sojoji suka kawo daga wani bangaren birnin ne dai ya taimaka daga karshen aka kori maharan kuma yanzu sojojin sintiri na bincike a wasu unguwannin da ke gabashin birnin inda ake sa tsammani can maharan suka buya bayan da suka gudu.

Kafin wannan rikicin da Ivory Coast ta samu cigaba sosai ta fuskar inganta tsaro tun bayan kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben kasar a bara.

Karin bayani