'yan fashi sun yi awo gaba da Naira miliyan 90 a kano

Image caption taswirar Najeriya

Wasu 'yan fashi da makami sun kai hari a fitacciyar kasuwar nan ta Kantin Kwari dake birnin Kano a arewacin Nigeria da yammacin ranar litinin.

'Yan fashin sun kwace kudadenda ake jin yawansu ya kai naira miliyan casa'in da 'yan kai kuma suka yi awon gaba da su.

Wani ganau yace maharan su shidda ne kuma sun zo ne akan babura dauke da manyan bindigogi; sai dai babu rahoton sun kashe wani.

Mai Magana da yawun 'yan sandan jihar Kanon ya ce 'yan fashin sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da jami'an tsaro sai dai kuma babu asarar rayukka.

Karin bayani