Ministan harkokin wajen Burkina Faso na ziyara a Arewacin Mali

Djibril Bassole Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Djibril Bassole

Ministan harkokin wajen Burkina Faso, Djibril Bassole, ya ziyarci arewacin Mali domin shiga tattaunawar tsakani da shugabannin 'yan tawaye masu tsattauran ra'ayin addinin Islama da suka kwace iko da yankin.

Wannan dai shine karo na farko da wata tawagar da aka nada daga yankin Afirka ta Yamma ke ziyartar kasar ta Mali kai tsaye.

Ba a dai cimma nasara a tattaunawar da aka yi a baya da 'yan tawayen a Burkina Faso ba,wadanda suka ce suna bukatar shari'ar musulunci ta yi karfi a mulkin kasar, suna masu cewa ba za su sassauta matsayinsu a kan wannan batu ba.

Babban jami'in hukumar da ke sa ido wajen tabbatar da shari'ar musulunci dake birnin Gao ya shaidawa BBC cewa batun har yanzu bai sauya ba.