BBC navigation

Bankin Standard Chartered ya musanta hada baki da Iran

An sabunta: 7 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:09 GMT

Wani sashen zauren Bankin Standard Chartered na Birtaniya

Bankin Standard Chartered na Birtaniya ya musanta zargin da Hukumar Kayyade Hada-hadar kudi a Amurka ta yi masa cewa ya hada baki da gwamnatin Iran domin boye wata hada-hadar kudi a tsakaninsu ta dala biliyan 250.

Hukumar ta Department for Financial Services DFS, wadda ke da hedikwata a birnin New York, ta ce bankin ya karya takunkumin yin hulda da Iran da Amurka ta sakawa masu hulda da ita, abin da ta ce ya sanya fannin hada-hadar kudi na Amurka cikin yiwuwar aibatawar 'yan ta'adda.

Hukumar ta DFS ta yi barazanar kwace lasisin bankin na yin hada-hada a Amurka saboda, a cewarta, ya hada baki da gwamnatin Iran inda suke hulda ta karkashin kasa fiye da shekaru goma.

Ta ce lamarin ya sanya tsarin kudin Amurka cikin halin da kasashe 'yan ta'adda da masu safarar kwayoyi da kuma masu almundahana ke iya yi musu illa.

Sai dai bankin ya ce rahoton hukumar ta birnin New York bai fadi ainihi da kuma cikakkiyar gaskiyar al'amarin ba, kuma ya nace cewa ya yi aiki sosai da takunkumin na Amurka.

Za a ba shi damar kare kansa

Za a bai wa bankin damar kare kansa a wajen wani zaman bahasi tsakaninsa da hukumar ta DFS nan gaba a cikin wannan watan.

Hukumar ta ce dole sai bankin ya kawo hujjar da za ta sa a bar shi ya ci gaba da gudanar da huldodinsa a birnin New York domin manyan shugabanninsa sun sani cewa ma'aikatansa na musanyar bayanan gaskiya dana karya.

Rasa lasisin gudanar da hada-hadar kudin a birnin New York dai wata babbar musiba ce ga wani bankin kasar waje; domin hakan na nufin ba shi da wata kafar shiga fannin hada-hadar bankuna na Amurka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.