Ana mummunan artabu a birnin Aleppo

aleppo Hakkin mallakar hoto afp
Image caption An kai hare hare da makaman roka a Aleppo

An fara gwabza wani kazamin fada tsakanin dakarun Syria da na 'yan tawaye a kokarin karbe iko da wata muhimmiyar anguwa a birnin Aleppo.

Kafafen yada labarun gwamnati na cewa sojojin kasar sun karbe iko da anguwar Salaheddine, wadda ita ce babbar matattarar 'yan tawayen a birnin, an kuma kashe 'yan tawayen da dama.

Sai dai 'yan tawayen sun musunta haka, sun kuma ce suna ci gaba da nuna tirjiya.

Wasu rahotanni na nuna cewa sai a daren ranar Talata ne Praministan Syria da ya sauya sheka ranar Lahadi, ya samu sukunin tsallaka kan iyaka zuwa cikin Jordan, bayan da aka rutsa da shi a kudancin kasar ta Syria.

Canza sheka

Kasar Jordan ta ce, tsohon Fira Ministan Syria, Riyad Hejab, ya tsallaka kan kasarta daga Syria, kwanaki biyu bayan da aka bayyana sauya shekar da yayi.

Sauya shekar tasa dai na nuna cewar, irin girman barakar da aka samu a gwamnatin Bashar al-Assad ta zarta yadda ake fadi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jordan ya shaidawa BBC cewa Mista Hejab da iyalansa sun ketara kan iyakar a daren jiya talata.

Masu fafitika a kasar Syria sun ce sai da iyalan nasa suka fake a wani gida dake kudancin kasar, kafin a fice da su waje.

Karin bayani