Za a kafa rundunar hadin gwiwa don samarda tsaro a Congo

congo Hakkin mallakar hoto x
Image caption Mutane na tserewa daga gabashin Congo

Shugabanni daga kasashen gabashi da kuma tsakiyar Afrika sun yanke shawarar duba yiwuwar kafa wata rundunar dakaru ta yanki, da nufin kawo karshen fada a gabashin Congo.

An zartar da shawarar hakan ne a lokacin wani taron koli wanda ba a dade da kammalawa ba a Uganda.

A yan watannin da suka wuce an rika tafka mummunan fada tsakanin 'yan tawayen kungiyar M23 da dakarun gwamnatin Congo.

Mutane kimanin dubu dari biyu ne suka ne fadan ya raba da muhallansu.

Kasashen da za su samar da sojojin kiyaye zaman lafiyar sun hada da Rwanda da Uganda da kuma Angola.

Dukansu dai sun kasance da hannu a yake-yaken da aka yi a baya a kasar ta Congo.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Rwanda da goyon baya ga 'yan tawayen kungiyar M23, wadanda ke da hannu a tashin hankali na baya-bayanan da aka yi a gabashin kasar ta Congo.

Sai da Rwandan ta musanta wannan zargi.

Karin bayani