Iran ta nemi a sa biki a sako yan kasarta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan Iran da aka kama

Iran ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta taimaka a sako 'yan kasarta arba'in da takwas da mayakan 'yan tawayen Syria suka kama a ranar Asabar.

Ministan hulda da kasashen waje na Iran, Ali Akbar Salehi, ne ya bukaci hakan a cikin wata wasika da ya aikewa sakatare janar na majalisar, Ban Ki-moon.

Iraniyawan na tafe ne cikin wata mota lokacin da 'yan tawayen Syria suka kama su bisa zargin 'yan leken asiri ne, koda yake Iran ta ce mutanen sun je ziyarar kaburburan waliyyan 'yan Shi'a ne da ke Syria.

Wakilin BBC yace ba'a dai tantance iyakacin goyon bayan da Iran ke yiwa gwamnatin Assad ba, sai dai rahotanni na cewa dakarun juyin-juya halin Iran na fafatawa a yakin da ake yi a kasar, na daga cikin dalilan da suka sa aka cafke 'yan Iran din arba'in da takwas.

Karin bayani