Sojin Masar sun harba makamai a Sinai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojin Syria

Jami'an tsaron Masar sun ce sojin kasar sun harba makamai masu linzami daga jiragen yaki bisa mayaka masu kishin Islama kusa da garin al-Arish da ke yankin Sinai.

Rahotanni sun ce kimanin mutane ashirin aka kashe a harin.

Shafin intanet na Ahram mallakar gwamnatin kasar yace an kai harin ne 'yan sa'o'i bayan da mayakan suka bude wuta kan wasu cibiyoyin bincike na jami'an tsaro guda uku da ke daura da iyakar Masar da Isra'ila da Gaza.

Harin na 'yan tada kayar baya ya biyo bayan wani harin a baya-bayan nan, inda aka kashe jami'an tsaron kan iyaka su goma sha shida a yankin.

Babu dai wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin, koda yake da Masar da Isra'ila na zargin mayakan Islama daga Sinai da takwarorinsu Palasdinawa daga zirin Gaza na kai hare-hare a yankin.

Karin bayani