An fara zaman makokin marigayi John Atta Mills a Ghana

Marigayi John Atta Mills Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marigayi John Atta Mills

An fara zaman makokin tsohon shugaban Ghana marigayi John Atta Mills wanda ya rasu a ranan 24 ga watan jiya, yana da shekaru 68.

Kwanaki uku ne dai za'a yi ana gudanar da zaman makokin kafin a yi jana'izarsa a ranar juma'a.

Dubun dubatan jama'a daga dukan sassan kasar da ma kasashen waje ne suke bin dogon layi don ziyartar gawar, wadda aka ajiye a babban zauren cin abincin kasar, watau Banquet Hall inda aka dauki kwararan matakan tsaro.

Daga wadanda ake san ran za su halarci makokin har da shugabannin kasashe goma sha shidda da kuma

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton.