Amnesty ta damu kan farar hula a Aleppo

Image caption Majalisar zartarwa ta Syria

Kungiyar kare hakkin Bil Adama, Amnesty International, ta ce tana cikin matukar damuwa game da halin da mazauna birnin Aleppo na Syria ke ciki bayan da hotunan tauraron dan adam suka nuna fiye da manyan ramuka dari shida a bayan garin.

Kungiyar ta ce tana zargin muggan makaman da dakarun 'yan tawaye dana gwamnati ke amfani da sune ke haddasa manyan ramukan.

Kungiyar ta yi gargadi ga bangarorin biyu cewa za ta rika adana bayanai a kan harin da aka kai wa fararen hula domin tuhumar wanda yake da hannu a ciki.

Ana ci gaba da artabu tsakanin dakarun gwamnatin Syria da na 'yan tawaye a birnin na Aleppo.

Karin bayani