An rufe bajakolin Afrika na gasar Olympics

Dandalin bajekolin kasashen Afrika a Olympic
Image caption Dandalin bajekolin kasashen Afrika a Olympic

An rufe dandalin da ya baje kolin kayan al'adun kasashen nahiyar Afrika da suka hallarci gasar Olympic saboda basussuka kamar yadda mai gana da yawun dandalin ya bayyana.

An kafa Africa village kamar yadda ake kiran dandalin a turance, a labun Kensington dake arewacin London.

Kuma masu kawo kayayyaki na bin bashin dubban fama-famai, inji Laurent Bagnis.

Kakakin ya kuma bayyana cewa kawo yanzu ba a tantance yawan bashin ba.

Ana yin wata ganawa don ganin cewa ko za a sake bude dandalin don baiwa kasar Tunisia damar baje nata kolin.

An yi niyyar yin wake-wake a ranar da aka warewa Tunisia.

Wannan ne karon farko da kwamitocin dake shirya gasar Olympics a kashen Afrika suka shirya irin wannan bajakolin.

Dandalin na kallon dakin taro na Royal Albert kuma yana da wajen bajekoli, sannan waje daya kuma ga gidan abinci da jama'a za su iya zuwa.

Haka kuma akwai zauren da jami'an gasar Olympics da 'yan wasu da masu daukar nauyinsu za su iya zama.

Tun lokacin da aka bude dandalin a ranar 28 ga watan Yuli, mutane dubu 80 sun ziyarci gurin, a cewar Mr. Bagnis.