Za mu taimakawa Najeriya da tsaro —Clinton

 clipn Hakkin mallakar hoto s
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Gwamnatin Amurka ta ce za ta taimaka wa Najeriya wajen fuskantar kalubalen da ke gabanta, ciki har da na tabarbarewar tsaro da matsalar cin hanci da rashawa.

Ta kuma ce makomar Najeriya za ta kasance kyakkyawa idan aka daidaita al’amura a kasar.

Kasar ta Amurka ta jaddada cewa akwai danganta mai karfi tsakaninta da Najeriya, kuma alakar na taimakawa wajen kyuatata harkokin noma da inganta ilimi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ce ta bayyana aniyar kasar tata a ziyarar da ta kai Najeriya.

Ta kuma kara da cewa: “Mun yi amanna cewa Najeriya na da kyakkywawar makomar da ba a san adadinta ba. Sai dai aikin da ke gabanku shi ne samar wa kowanne dan kasa damar habaka da bunkasa, ta yadda kowa da kowa—babba da yaro—zai samu cin gajiyar baiwar da Allah Ya yi masa.

“Saboda haka za mu goya muku baya wajen yanke muhimman shawarwari a rayuwa”.

Duk da cewa Sakatariyar Harkokin Wajen ta Amurka ta gana da shugaban Najeriya a asirce, wata majiya ta ce gwamnatin Amurka ta yi wa Najeriya tayin tallafa mata wajen tsara dabarun tsaro da nufin magance rikice-rikicen da take fama da su, wadanda suka hada da hare-haren ’yan bindiga da bama-bamai.

Amurka ta ce agaza wa Najeriya ya zama wajibi saboda kasar tana da muhimmanci a nahiyar Afirka, da musamman shiyyar Afirka ta Yamma, wajen wanzar da zaman lafiya.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ce Amurka da Najeriya na karuwa da juna sakamakon huldar da suka kulla da juna, wadda ta nan ne suke duba muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar junasu.

“Muna tattaunawa a kan abubuwa da dama da suka hada da tsaro da tattalin arziki da sauransu, kuma kuna matukar taimaka mana”, inji Mista Jonathan, wanda ya kara da cewa, “Haka kuma gwamnatin Shugaba Obama na ji da nahiyar Afirka, da kuma Najeriya. Kun dade kuna tallafa mana, musamman ma yadda kuka tsaya mana lokacin rasuwar Marigayi Shugaba ’Yaradua, wajen samar wa Najeriya mafita daga rudanin da ta fuskanta”.

Hakazalika Sakatariyar Harkokin Wajen ta Amurka ta gaggana da wadansu ministoci wadanda suka hada da ta kudi, da ta mai, da na wutar Lantarki, da na harkokin waje, da kuma Majalisar Tsaron Kasa, nan ma a asirce.

Najeriya dai na fama da rikice-rikice, inda ake kai hare-haren bindiga da bama-bamai, wadanda ke sanadin mutuwar mutane da dama da kuma asarar dukiya, musamman a arewacin kasar—hare-haren da kungiyar Jama’atu Ahlis-Sunnah lid-Da’awati wal-Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram ta dauki alhkin kai wadansu daga ciki.

Haka kuma Najeriya na cikin kasashen da ke da arzikin mai a duniya, kuma kasar Amurka na cikin masu sayen mai daga hannunta.

Sai dai mafi yawan al’ummar kasar na fama da talauci sakamakon matsalar cin hanci da rashawa da ta mamaye harkokin rayuwa a kasar, inda a lokuta da dama aka zargi wadansu jami’an gwamnati da manyan ’yan siyasa da kuma makusantansu, amma ba kasafai ake hukunta su ba.

Kodayake hukumomin da ke yaki da cin hanci a kasar na alwashin kawo karshen al’amarin, saboda a halin da ake ciki ana kan shari’ar wadansu da ake zargin sun yi almundahana a shirin bayar da tallafin man fetur a kasar.

Karin bayani