Clinton na ziyara a Najeriya

 clipn Hakkin mallakar hoto s
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, na yin ziyara a Najeriya domin ganawa da shugaban kasar da sauran jami'an gwamnati.

Ana sa ran ziyarar za tabo al'amuran tsaro da cin hanci da rashawa da suka yi wa kasar katutu.

Mrs Clinton za ta tattauna da shugaban kasarGoodluck Jonathan game da hare-haren da kungiyar Ahlissunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ke yawan kai wa a kasar.

Alaka tsakanin kasashen biyu dai na da karfi, kasancewar Najeriya ce kan gaba a Afrika wajen sayarwa Amurka man fetur.

Sakatariya Clinton za kuma ta tattauna da hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya.

Kiraye-Kiraye

Tuni dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta yi kira ga sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da ta yi amfani da ziyarar wajen kira ga hukumomin kasar su gaggauta daukar mataki a kan karuwar kashe-kashen da ake fama da su a kasar.

Kungiyar ta yi wanna kiran ne a wata wasika da ta aike wa Hillary Clinton.

Ziyarar ta Hillary Clinton na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da ake kaiwa a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.

Human Right Watch ta ce ya kamata Misis Clinton ta karfafawa shugaban Najeriya Goodluck jonathan gwiwa dan kawo karshen tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta,wanda yawanci kungiyar Boko Haram ke daukar alhakin kaisu.

Kungiyar ta ce rayukan musulmai da kiristoci da dama ne suka salwanta a cikin shekaru hudu da suka wuce a yankunan da suka fi fuskantar tashe-tashen hankula a Arewaci da tsakiyar Najeriya.

Karin bayani