Shugaba Mursi ya kori Field Marshal Tantawi

Shugaba Mursi da Field Marshal Tantawi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammad Mursi na Masar da Field Marshal Hussein Tantawi suna kus-kus

Shugaban Masar, Muhammad Mursi, ya kori ministan tsaron kasar mai karfin fada-a-ji, Field Marshal Hussein Tantawi—shi da mataimakinsa.

Shugaba Mursi ya kuma soke sauye-sauyen da sojoji suka yi ga kundin tsarin mulki wadanda suka takaita ikon shigaban kasa.

Kakakin shugaban kasar, Yasir Ali, shi ne ya bayar da sanarwar ta gidan talabijin.

“Shugaban kasa ya zartar da kudurori kamar haka: na farko, ya soke dokar tsarin mulki ta wucin-gadi wacce aka ayyana ranar 17 ga watan Yuni; na biyu, ya ba da umurnin yi wa Field Marshal Muhammad Hussain Tantawi Sulaiman ritaya a matsayinsa na babban hafsan soji kuma ministan tsaro daga yau”, inji kakakin.

Bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak dai bara, Field Marshal Tantawi ne ya karbi jagorancin gwamnatin kasar.

Kafin nan shi ne yake rike da mukamin ministan tsaro.

Wakilin BBC a kan al'amuran Gabas ta Tsakiya ya ce Misrawa za su kalli wannan sanarwa a matsayin wani muhimmin mataki a fafutukar da ake yi ta damke hakikanin madafun iko.

Karin bayani