Ana taro a kan matsalar yunwa a London

David Cameron Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Cameron

Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron, yana karbar bakuncin wani taro a kan yadda za a tunkari matsalar yunwa a duniya a London.

Mista Cameron dai na fatan tara isassun kudaden da ake bukata ne don hana kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar fama da karancin abinci mai gina jiki nan da Gasar Olympics ta 2016 a Brazil a matsayin wani abin tarihi da Gasar Olympics ta London ta gadar.

Duncan Green jami'i ne a kungiyar bayar da agaji ta Oxfam, ya kuma shaidawa BBC cewa Birtaniya na so ne ta yi amfani da wannan dama don wayar da kai dangane da matsalar ta yunwa:

“Ina ganin wannan taro ya dace kasancewar za a tara al'ummar duniya don su gudanar da wani muhimmin al'amari”, in ji Mista Green.

’Yan siyasa daga Brazil da Kenya da Bangladesh da ma wadansu fitattun 'yan wasa suna halartar taron.