Ruwa ya share kauyuka a Filaton Najeriya

Wasu daga cikin gidajen da ruwa ya rusa a Jos Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu daga cikin gidajen da ruwa ya rusa a Jos kwanan baya

Rahotanni daga Jihar Filato a Najeriya sun ce wata mummunar ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da kauyuka da kuma garuruwa da dama a kananan hukumomin Langtang da Wase bayan da aka kwana ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Rahotannin daga kudanci da tsakiyar jihar sun kuma ce an samu dimbin ta’adi na gidaje da gonaki da sauran kadarori kuma ana ma fargabar an samu asarar rayuka sakamakon ambaliyar.

John Bull Sule, wani mazaunin garin Langantan ne kuma ya shaida wa wakilin BBC Is’haq Khalid cewa bayan da aka kwana ana ruwan a kananan hukumomin Lantang ta Arewa da Langtanag ta Kudu, dimbin gidaje sun salwanta, abin da ya jefa jama’a cikin halin kaka-ni-ka-yi.

“Barnar ta wuce misali; mutane sun rasa matsugunai da yawa—idan na ce maka za a iya kidaya [yawan gidajen da aka rasa] karya nake yi maka”, inji John Bull.

Dangane da asarar rayuka kuwa, cewa ya yi sai dai nan gaba za a iya tantancewa, saboda “ruwan da aka fara kamar Ruwan Dufana tun karfe goma sha biyu dare har wayewar gari—ruwa ya tafi da mutane amma ba a tabbatar ko wa da wa [ya tafi da su] ba”

Shi ma wani mazaunin Wase, Alhaji Hamisu Wamba Wase, ya ce a karamar hukumarsu jama’a sun dimauce yayin da ruwan ya dirkake su, kuma kawo yanzu ba a iya tantance yawan ta’adin da ya yi ba.

A cewarsa, “Yawancin mutane a kan bishiyoyi ma suke. Duk wanda ya fada ma [yawan asarar da aka yi] yanzu haka sai dai ya fadi abin da ranshi yake so, don ba wanda ya iya kaiwa wurin—abin ya shafi akalla kauyuka ashirin zuwa talatin”.

A karamar hukumar Kanam ma rahotanni daga yankin Garga na cewa gidaje kimanin dari biyu sun salwanta wata budurwa kuma ta rasa ranta.

Alhaji Sadat Garga shi ne dan majalisar dokokin jihar Filato mai wakiltar mazabar Kantana inda yankin na Garga yake:

“Ko da yake mutane sun koma wurin ’yan uwansu wadanda ambaliyar ba ta shafe su ba ana nan a cikin halin ha’ula’i—ba agaji ko daya zuwa yanzu. Mun fada wa hukmomin da abin ya shafa, kamar [Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya, wato] NEMA da Hukumar Agajin Gaggawa ta jiha”, inji Alhaji Sadat.

Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar, Alhaji Alhassan Barde, ya ce suna shirin hadin gwiwa da hukumomin tarayya da na kananan hukumomi da nufin tantance ta’adin da aka samu da kuma bayar da taimako.

Wannan ambaliya dai na zuwa ne bayan da wata ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da arba’in a Jos, babban birnin jihar a ’yan kwanakin da suka gabata.

Dama dai hukumomi sun yi hasashe da kuma gargadin cewa za a yi fama da ambaliya a jihohi da dama na Najeriya cikin har da jihar ta Filato daga watan Agusta zuwa Oktoba.

Sai dai kuma abin da ya fi tayar da hankali a cewar masu lura da al’amura shi ne kawo yanzu babu wani kwakkwaran matakin kariya da aka dauka a zahiri daga bangaren su jama’a da kuma hukumomi.

Karin bayani