Samfuran dan adam da dama ne suka rayu a Afirka

Image caption Kokon kan mutum

Masu binciken kimiyya sun ce wasu kasusuwa da aka hako a arewacin Kenya sun nuna cewa wani samfurin halittar dan adam ya rayu shekaru miliyan biyu da suka gabata.

Wannan sabon binciken ya nuna cewa samfurin bil adama uku ne suka rayu a nahiyar Afirka.

Binciken ya kara adadin hujjoji da suka musanta hasashen da aka yi cewa biri ne asalin dan adam.

An wallafa sakamakon binciken ne a mujallar kimiyya ta Nature.

Masu nazarin dabi'ar dan adam sun gano kasusuwan mutane uku da suka rayu tsakanin shekaru miliyan daya da dubu dari bakwau zuwa miliyan daya da dubu dari tara da suka wuce.

Kasusuwan na fuska guda ne da kuma mukamiki guda biyu hade da hakora.

Babu kamarsa

Kasusuwan sun tabbatar da ra'ayin cewa kokon kan da aka gano a 1972 na samfurin bil adam ne daban wanda a kimiyance ake kira Homo rudolfensis.

Kokon kan ya sha bamban da sauran wadanda aka gano a wancan lokacin domin yana da babbar kwakwalwa da doguwar fuska faffada.

Sai dai tsawon shekaru 40, ba a samu wani kokon kan da ya yi kama da irin wannan ba, abin da yasa aka kasa tantance ko sabuwar halitta ce ta daban ko kuma bare ne a cikin halittar da aka saba da ita.

Yanzu da yake an gano wadannan kasusuwa guda uku, manazarta na iya bugar kirji su tabbatar da cewa Homo rudolfensis samfurin halittar dan adam ne na daban, wanda ya rayu kimanin shekaru miliyan biyu da suka wuce tare da sauran halittun bil adama.

A baya dai an kwashe lokaci mai tsawo ana tunanin cewa mafi dadewar samfurin halittar dan adam a duniya ya rayu ne shekaru miliyan daya da dubu dari takwas da suka wuce.

Irin wannan samfurin halitta mai karamin kai da katon goshi, wanda ke iya mikewa tsaye shi ne masana ke kira Homo erectus.

Bambance-bambance

Sai dai shekaru 50 da suka wuce, masanan sun gano wani samfurin halittar wanda yafi wannan dadewa da suka yi wa lakabi Homo habilis, wanda mai yiwuwa ya yi zamani da Homo Erectus.

A yanzu kuma an gano cewa shima H. rudolfensis ya rayu tare da su, abin da ke nuna cewa akwai yiwuwar akwai wasu samfuran halittun dan adam da dama da ba a ma kai ga gano su ba tukunna.

Wannan hujja ta baya-bayan nan na kalubalantar hasashen da aka yi a baya cewa dan adam ya samo asali ne kai tsaye daga birrai.

Sai dai a cewar Dr Meave Leakey, na cibiyar Turkana Basin da ke Nairobi, wacce ta jagoranci binciken, hakan ya nuna cewa an samu bambance-bambance a tarihin samuwar dam adam.

Ta shaidawa BBC cewa: '' Akwai bambance-bambance masu yawa a asalin faruwar dan adam. Babu wani muhimmin abu game da kakannin kakanninmu har sai da suka fara sassaka duwatsu domin samar da kayan amfanin yau da kullun.

Da ma a tarihin sauran dabbobi suna samar da samfuran halitta daban-daban kamar su launin gashi ko kirar baki ne a lokuta mabambanta. Idan sabon samfurin ya dace da muhallin da suke sai su ci gaba da rayuwa; idan bai dace ba kuma sai su kare.

A cewar Farfesa Chris Stringer na Gidan ajiye kayan tarihin halitta da ke London, shaidar kasusuwan na kara tattabatr da cewa samuwar dan adam ta biyo irin wannan tsarin ne.

Karin bayani