'Yan gudun hijirar Syria na karuwa matuka

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Syria

Hukumar da ke kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana samun karuwar ’yan kasar Syria da suke gujewa yankunan da ake tafka gumurzu, musamman daga birnin Aleppo.

Hukumar ta ce ta yiwa kusan mutane dubu dari da hamsin rajista a kasashe hudu masu makwabtaka da kasar ta Syria.

Haka kuma Amurka ta ce za ta kara yawan tallafin jin kai da take baiwa ’yan gudun hijirar na Syria da kimanin dala miliyan biyar da dubu dari biyar.

Jami’an Amurka sun ce za a sanar da sababbin takunkumi a kan Shugaba Bashar al-Assad da makusantanshi, ciki har da ministocinsa.

Tun da farko Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya William Hague ya bayar da sanarwar agajin da y ace ba na makamai ba wanda ya kai kusan dala miliyan takwas.

Karin bayani