Ana ci gaba da kazamin fada a Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Aleppo a Syria

Ana cigaba da kazamin yaki tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a Aleppo, birni na biyu a kasar Syria.

Kafafen yada labaran gwamnatin Syria na cewa soji sun kwace unguwar Salaheddin wacce a da ta ke hannun 'yan tawaye.

Sai dai 'yan tawayen sun ce sun sake kai hari a yankin.

Rahotanni dai na cewa an kwana ana dauki-ba-dadi a sassa daban-daban na garin Aleppo yayinda bangarorin biyu ke kokarin kare wuraren da ke karkashin ikonsu.

Karin bayani