'Yan tawayen Syria sun janye daga Salaheddin

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Aleppo a Syria

Rahotanni daga birnin Aleppo na Syria na cewa babbar rundunar mayakan 'yan tawaye ta janye mayakanta daga matattararsu dake can, bayan wadansu hare-haren bam daga dakarun gwamnati.

Wani dan jaridar Birtaniya a birnin na Aleppo ya ce an bayar da umurnin janyewa daga unguwar Saleheddine ne bayan da jiragen yakin gwamnati da tankokin yaki suka kwashe dare suna kai hare-hare ba kakkautawa a kan wurare uku na 'yan tawayen.

Rundunar 'yan tawayen ta Free Syrian Army ta ce ta janye ne domin kara kintsawa, amma rahotanni na cewa dakarun gwamnati sun shiga unguwar.

Gwamnatin kasar ta Syria dai na amfani da dukkan abubuwan da take iya yin amfani da su domin ganin ta fitar da 'yan tawayen.

Yanzu dai unguwar Saleheddine ta fita daga hannun 'yan tawayen, kuma mayakan 'yan tawayen sun koma yankin kudu maso yammacin birnin Aleppo domin ci gaba da fuskantar sojojin gwamnati.

Sai dai har yanzu ba a iya cewa an dakatar da fada a cikin birnin. Daga yankin kudu, unguwar Sukkari da kuma unguwar Seif al Dawla a yamma, suna hannun 'yan tawaye.

Kafofin yada labarai mallakar gwamnati na cewa dakarun gwamnati sun kashe da dama wadanda suke kira 'yan ta'adda.

A halin da ake ciki kuma, Shugaba Assad ya nada ministan kiwon lafiya Wa'il al Halqi a matsayin Firayim Ministan kasar domin maye gurbin Riyad Hijab wanda ya sauya sheka ya koma bangaren 'yan tawaye.

Karin bayani