An mika mulki ga Majalisa a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Libya

Gwamnatin rikon kwaryar Libya ta mika mulki ga sabuwar zababbiyar majalisar dokoki ta kasar a wani biki da aka gudanar a Tripoli, babban birnin kasar.

Wannan ne karo na farko da aka mika mulki ga zababbiyar gwamnati bayan hambarar da kanal Ghaddafi a bara.

Dubban 'yan kasar ne suka kwarara kan titunan babban birnin Tripoli, don nuna murnar su da mika mulkin.

A bara a irin wannan lokacin ne dai masu adawa da gwamnatin Ghaddafi suka mamaye birni Tripoli, kuma suka tilastawa tsohon shugaban barin birnin daga bisa ni suka kashe shi.

Karin bayani