Amurka ta kara kakaba wa Hizbullah takunkumi

Mayakan kungiyar Hizbullah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta zargi mayakan kungiyar Hizbullah da taimakawa dakarun Syria

Amurka ta zargi kungiyar Hizbullah mai gwagwarmaya da makamai a Lebanon da bayar da horo, da shawarwari, da kuma tallafi ga gwamnatin Syria a yunkurinta na murkushe ’yan adawa.

Ta kuma zargi kungiyar ta Hizbullah da taimaka wa Dakarun Juyin Juya-Hali na Iran, wato Revolutionary Guard, wajen bayar da horo ga dakarun Syria.

Tuni dai Washington ta ayyana Hizbullah a matsayin kungiyar ’yan ta’adda, ta kuma sanar da kakaba mata sababbin takunkumi.

Sai dai kuma wakilin BBC a Washington ya ce wannan takunkumi na je-ka-na-yi-ka ne saboda kungiyar ta Hizbullah ba ta da kadara a Amurka.

Kakakin Fadar Gwamnatin Amurka ta White House, Jay Carney, ya ce “Abin da muke son cimmawa shi ne mu ci gaba da matsawa gwamnatin Assad lamba, mu ci gaba da mayar da ita saniyar-ware, mu kuma nuna cewa abokan Shugaba Assad kalilan ne suka rage—wato Iran da Hizbulla”.