Yan sanda a Sin an zarge su da rufa rufa

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Gu Kailai

A ranar Juma'a wata kotu dake kasar China za ta saurari shari'ar wasu 'yan sanda guda hudu da ake tuhuma da laifin yin rufa-rufa game da kisan kan da ake zargin Gu Kailai, matar dan siyasar da aka daina damawa da shi Bo Xlai da aikatawa.

Ana dai tuhumar 'yan sandan ne da karya doka tare da son kai ta hanyar kokarin kare Gu Kailai daga bincike bayan mutuwar Neil Heywood wani abokin kasuwancin Mrs. Gu dan kasar Burtaniya.

A ranar Alhamis ne aka saurari shari'ar Gu Kailai sai dai ba'a bayyana ranar da za'a yanke mata hukunci ba.

Kasashen duniya na sa ido kan shari'ar saboda Bo Xlai mijin matar da ake tuhuma babban jami'in Jamiyyar gurguzu ne na kasar ta China.

Karin bayani