Japan ta ja kunnen shugaban Korea ta Kudu

Tsibiran Dokdo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsibiran Dokdo

Japan ta yi gargadin cewa ziyarar da Shugaba Lee Myung-bak na Korea ta Kudu ya kai tsibiran Dokdo za ta yi illa ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Lee ne dai shugaban kasar Korea ta Kudu na farko da ya kai ziyara zuwa tsibiran—wadanda a Japan aka sansu da suna Takeshima—wadnda ake takaddama a kansu.

Ziyarar ta zo ne kwanaki biyar kafin bikin cika shekaru sittin da bakwai da kawo karshen Yakin Duniya na Biyu, lokacin da Korea ta Kudu ta samu 'yancin kai daga mulkin mallakar Japan.

Wadansu mazauna Seoul sun bayyana ra’ayoyinsu game da ziyarar.

A cewar mutum na farko, “Wannan ziyara ba wani abu ba ne”, yayin da wata mata ta ce, “Ziyarar za ta harzuka Japan—za a samu matsalar diflomasiyya tsakanin kasahen biyu”.

Japan ta fusata da ziyarar kuma tana shirin kiran jakadanta daga Seoul.

Kafofin yada labarai na kasar ta Japan sun bayyana ziyarar da cewa wani yunkuri ne na ganin ya samu goyon baya daga masu kada kuri’a lokacin zabe.

Farin jininsa dai ya ragu tun lokacin da aka tsare dan uwansa a bisa zarge-zargen cin hanci.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ziyarar Shugaba Lee Myung-bak zuwa tsibiran Dokdo ta jawo ce-ce-ku-ce

Takaddamar da ake yi game da wadannan tsibiran ta jima, tana kuma kawo tangarda a dangantaka tsakanin Japan da Korea ta Kudu.

Tsibiran dai na wani wuri ne mai arzikin kifi kuma akwai dimbin arzikin iskar gas a yankin.

Kasashen biyu dai sun shafe shekaru aru-aru suna ikirarin mallakar tsibiran amma Korea ta Kudu ce ke da iko da su tun shekarar 1953.

Wannnan batu dai ya rikide zuwa rikici a shekarar 2005.

A lokacin da jakadan Japan a Seoul na wancan lokacin ya nanata ikirarin Tokyo, masu zanga-zanga a Korea ta Kudu sun yi ta bankawa kansu wuta suna kashe kansu.

Karin bayani