Myung-bak na Koria ya kai ziyara tsibirin da ake takaddama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matatar man Koriya

Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Myung-bak ya zamo shugaban kasar na farko da ya kai ziyara kan wasu tsibirai da Koriya ta Kudu da Japan ke takaddama game da mallakarsu.

Mr. Lee ya kai ziyarar ne duk da gargadin da Japan ta yi cewa hakan zai iya kawo mummunan sabani tsakaninsu.

Tsibiran da 'yan Koriya ke kira Dokdo, Japanawa kuma ke kiransu Takeshima na karkashin ikon Koriya ta kudu tun alif da dari tara da hamsin da uku.

Tsibiran dai na tsakiyar teku ne mai albarkar kifaye kuma ana hasashen cewa za'a iya samun iskar gas a yankin.

Karin bayani