'Yan bindiga sun harbe wani janar a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana taya Mogaref murna

Wasu 'yan bindiga a Libya sun harbe wani babban janar na soji har lahira a garin Benghazi da ke gabashin kasar.

Janar Muhammad Hadiyah shi ne ke kula da makamai a ma'aikatar tsaron Libya kuma ya na dawowa daga masallaci ne wasu mutane hudu su ka tare shi a cikin mota.

Dan marigayin ya ce sai da aka nemi janar din da ya baiyana kan sa kafin a harbe shi.

Janar Hadiyah dai na daga cikin manyan sojin da suka fara marawa 'yan adawa baya a boren da aka yi a bara.

Kawo yanzu dai ba'a gano musabbabin kashe shi ba.

Karin bayani