Clinton za ta gana da gwamnatin Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton na ziyarar kasar Turkiyya domin tattaunawa game da rikicin Syria mai makwabtaka da ita.

Za ta gana da shugaban kasa da kuma Piraministan Turkiyya domin shirya matakan taimakawa 'yan tawayen Syria da kuma yadda za'a tafiyar da kasar bayan hambarar da shugaba Assad daga karagar mulki.

Kawo yanzu dai fiye da 'yan Syria dubu hamsin ne ke gudun hijira a Turkiyya kuma ana sa ran Mrs Clinton za ta bada agaji daga gwamnatin Amurka.

Kasar Syria dai na ta artabu da yan tawaye inda take son murkushe masu adwara dauke da makamai, 'yan adawar kuma na son hambarar da gwamnatin shugaba Assad.

Karin bayani