'Mun kashe 'yan Boko Haram 20'-Sojoji

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO YOUTUBE
Image caption Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram

Jami'an tsaro a jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun ce sun kashe 'yan kungiyar Ahlussuna Lidda'wati Waljihad da aka fi sani Boko Haram guda 20 ranar Lahadi.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin-gwiwa JTF a jihar, Kanal Victor Ebhaleme, ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun budewa sojoji wuta a lokacin da sojojin suka doshi wajen da 'yan kungiyar ke yin taro a birnin, lamarin da ya sanya aka yi bata-kashi a tsakaninsu.

Kanal Ebhaleme ya kara da cewa a sanadiyar wannan bata-kashi ne aka kashe 'yan kungiyar guda ashirin sannan su kuma suka kashe soja daya.

Wani kakakin kungiyar da ake kira Boko Haram din ya musanta labarin da rundunar sojin ta bayar inda ya ce wadanda aka kashe fararen hula ne.

Ya kara da cewa ba zai yiwu ba 'yan kungiyar su ashirin su taru waje guda don gudanar da wani taro.

A jihar Yobe ma, rundunar tsaro ta JTF ta tabbatar cewa ta kashe 'yan bindiga guda biyu sannan ta kama mutane 30 da take zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne a Damaturu, babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce an shafe kusan yinin ranar Lahadi ana jin karar tashin bindigogi a birnin na Damaturu.

Mazauna birnin, wadanda wasunsu suka tsere suka shiga daji, sun ce tun da sanyin safiyar ranar ne jami'an rundunar tsaro ta hadin-gwiwa suka kewaye wasu unguwanni suna shiga gida-gida suna kama mutane.

Karin bayani