Damaturu: anyi harbe-harbe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren da aka a baya a Damaturu

Rahotanni daga jihar Yobe a arewacin Najeriya sun ce an shafe kusan yinin yau ana jin kaarar tashin bindigogi a Damaturu babban birnin jihar.

Mazauna birnin wadanda wasun su suka tsere suka shiga daji, sun ce tun da sanyin safiyar yau jami'an rundunar tsaro ta hadin-gwiwa suka kewaye wasu unguwanni suna shiga gida-gida suna kama mutane.

Mazauna garin na Damaturu da dama ne suka tsere tun daga lokacin da aka soma yada jita-jitar yiwuwar kai hare-hare a lokacin bukukuwan sallah dake tafe.

Garin na Damaru dai ya sha fama da hare-haren da ake dangantawa ga kungiyar nan da ake kira Boko Haram.