Barnar da girgizar kasa ta yi a Iran

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutanen da girgizar kasar Iran ta raba da gidajensu

Masu aikin ceto na can suna tona baraguzan gine-ginen da suka rufta don kokarin ceto mutanen da suka rayu a girgizar kasa a Iran wadda ta yi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da 200.

Girgizar kasar ta auku ne a kauyukan birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar.

Kauyuka shida ne suka rufta baki daya, yayin da wasu kimanin sittin suka yi matukar lalacewa.

Dubban mutane ne suka kwana a tsaye sakamakon irin kaduwar da suka yi bayan girgizar kasar.

Agajin gaggawa

Masana a kan yadda kasa ke motsi na jami'ar Tehran sun ce girgizar kasar ta auku ne sau biyu 'yan mintuna tsakanin juna.

Rahotanni na cewa aukuwar girgizar kasar ke da wuya jama'ar birnin Tabriz suka hau kan tituna saboda tsabar kidimewa.

Harkokin sufuri sun tsaya cik a yankin, a yayin da masu kai agajin gaggawa ke kokarin zuwa wuraren da lamarin ya fi yi wa barna.

Alkaluman da shugaban cibiyar da ke kula da aukuwar masifu a yankin, Khalil Saie, ya bayar sun nuna cewa mutane dari biyu da hamsin ne suka hakala.

Sai dai da wuya a san irin barnar da girgizar kasar ta yi kasancewa kauyukan na da wahalar shiga.

Hukumomi a kasar sun ce ana yin amfani da jirage masu saukar ungulu domin isa wuraren da girgizar kasar ta shafa, inda aka kai wa mutanen tantuna da biredi da kuma ruwan sha.

Karin bayani