Cameron ya karbi bakuncin taro a kan yunwa

David Cameron Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firayim Ministan Birtaniya David Cameron

Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron, ya karbi bakuncin wani babban taro a kan yadda za a tunkari matsalar yunwa a duniya a matsayin wani abin tarihi da Gasar Olympics ta London za ta gadar.

Mahalarta taron sun hada da shahararrun ’yan wasa, ciki har da dan tseren nan na Birtaniya wanda ya lashe lambobin zinare, Mo Farah, da shugabannin siyasa, da kungiyoyin agaji, da kuma wakilan ’yan kasuwa.

Mista Cameron ya yi kira ga kasashen duniya su dauki kwakkwaran mataki don kawo sauyi a rayuwar miliyoyin yara.

“Lallai ne mu rika cika alkawuran da muke dauka idan mun yi tarurruka irin wannan—ya kamata a rika zube-ban-kwarya wajen adana bayanan ci gaban da ake samu a kuma rika samar da wadannan bayanai ga al'ummarmu saboda su rika bibbiyar abin da gwamnatoci suka ce za su yi da kuma hakikakin abin da suke yi”, inji Mista Cameron.

Manufar taron dai ita ce tara isassun kudaden da ake bukata don hana kananan yara ’yan kasa da shekaru biyar fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki kafin gasar Olympics ta shekarar 2016 a Brazil.

Karin bayani