Taron kasashen Larabawa a kan Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mambobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa a lokacin da suke yin taro

A ranar Lahadi ne ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ke ganawa a birnin Jedda na kasar Saudiyya don tattaunawa game da rikicin Syria.

Ana sa ran ministocin za su tattauna a kan mutumin da ya kamata a nada domin maye gurbin Mista Kofi Annan, wakilin kasashen duniya a kasar Syria, wanda ya sanar da yin murabus dinsa a farkon watan nan.

Rahotannin sun ambato mataimakin Sakatare Janar na kungiyar, Ahmed Ben Helli, na cewa mai yiwuwa tsohon ministan harkokin wajen Algeria, Lakhdar Brahimi, ne zai maye gurbin Mista Annan.

Brahimi dai ya wakilci Majalisar Dinkin Duniya a kasashe da dama ciki har da Afghanistan, da Iraq da kuma Sudan.

Ben Helli ya kara da cewa sun gayyaci shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad, wanda babban aboki ne ga shugaba Assad, wajen taron.

Taron ministocin wajen dai yana zuwa ne bayan ganawar da Sakatariyar harkokin wajen Amurka ta yi da takwaranta na kasar Turkiya game da yadda za a shawo kan rikicin kasar Syria.

Da ma dai wa'adin aikin wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syria zai kawo karshe nan da mako guda.

Karin bayani