Morsi na neman goyon bayan Misrawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Morsi da Tantawi da kuma wasu jami'an gwamnatin Masar

Shugaban kasar Masar, Mohamed Morsi, ya yi kira ga 'yan kasar da su goya masa baya, bayan da ya sauke shugaban rundunar sojin kasar mai karfin iko.

'Yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood sun jinjinawa matakin da Morsi ya dauka na cire shugaban sojin, Mohamed Hussein Tantawi.

Da dama daga cikin 'yan kasar sun ce cire Tantawi ya zama cikamakin juyin-juya halin da aka yi a kasar.

Shugaba Morsi ya rusa dokar da sojojin kasar suka yi wacce ta takaita ikon gwamnatin farar hula, kana ta bai wa sojoji cikakken iko.

Mista Morsi ya ce ya dauki matakin ne ba domin ya batawa wani rai ba.

Mista Tantawi ya karbi ikon tafiyar da kasar ne bayan hambarar da shugaba Hosni Mubarak daga kan mulki a shekarar da ta gabata.

Karin bayani