'Yan sanda a Norway sun yi sakacin hana kashe mutane 77

Anders Behring Breivik Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anders Behring Breivik da lauyansa suna ganawa

Wata hukuma a Norway dake binciken yadda 'yan sandan kasar suka maida martani game da hare-haren da Anders Behring Breivik ya kai a bara, ta gano cewar da 'yan sandan sun yi abinda ya kamata da an hana aukuwar harin.

Hukumar dake binciken ta kuma ce, da hukumomin tsaro sun yi abinda ya dace da ma an kama Breivik tun ma kafin ya kai ga aikata kisan mutane saba'in da bakwai.

Aleksandra Bech, shine ya shugabanci hukumar data gudanar da binciken, ya kara da cewar "hukumomi sun gaza wajen kare mutanen tsibirin Utoeya".

Dan Kasar ta Norway dai, ya amince cewar ya hallaka mutane 77, ya kuma jikkata sama da mutum 240, a lokacin daya tayarda bam a Oslo. Sai kuma harbe harben da yayi a tsibirin Utoeya.

Za a yanke masa hukunci a shari'ar da ake yi masa cikin wannan watan

Karin bayani