An kammala gasar Olympics

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mawaka rike da tutoci a lokacin kammala gasar Olympic

An mika tutar gasar Olympics ga birnin Rio de Janeiro wanda zai karbi bakuncin gasar a shekarar 2016 bayan rufe wasannin da wani gagarumin biki a birnin London.

Bikin rufe gasar, wanda aka yi a filin wasan Olympics, ya samu halartar manyan mawakan Birtaniya kamar Beatles, da Queen da Oasis.

Shugaban kwamitin shirya wasan Olympics na duniya, Jacques Rogge, ya bayyana wasan na London da cewa na farin ciki ne kuma mai gamsarwa.

Magajin birnin Rio, Eduardo Paes, ya shaidawa BBC cewa gasar Olympic da aka gudanar a London ta kasance wata abar koyi.

Wannan shi ne karon farko da Brazil za ta dauki bakoncin gasar, sai dai tuni aka fara bayyana fargaba kan kasar na yiwuwar iya daukar gasar saboda ba ta shirya a kan lokaci ba.

Karin bayani