Syria: an harbo jirgin gwamnati

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin saman yaki na Syria da aka harbo

Mayakan 'yan tawayen Syria, sun ce sun harbo wani jirgin yakin gwamnati kusa da kan iyakar kasar da Iraqi.

Hotunan da aka sanya a shafin Internet sun nuna wani jirgi yana cin wuta, bayan karar harbin bindiga.

'Yan tawayen sunce sun kama matukin jirgin.

Wani bidiyo ya nuna wani mutum yana cewa ya samu rauni, amma wadanda suka kama shi, suna masa magani.

Gidan talabijin na Syria dai ya tabbatar da cewa jirgin ya yi hatsari, amma yace sakamakon wata matsala ce da jirgin yaci karo da ita.

Wani wakilin BBC a yankin yace idan har aka tabbbatar da cewar harbo jirgin aka yi, to hakan na nufin an shiga wani sabon babi ke nan a rikicin Kasar ta Syria.